An nuna juyayi ga waɗanda suka rasu a haɗarin jirgin saman MU 5735

Daga CMG HAUSA

A yammancin yau Lahadi 27 ga wata, an nuna juyayi ga waɗanda suka rasa rayuka a haɗarin jirgin sama mai lamba MU5735 na kamfanin China Eastern Airlines wanda ya faru a ranar 21 ga watan Maris da muke ciki a filin da aka gano jirgin, inda mamban majalisar gudanarwar ƙasar Wang Yong ya halarci taron.

Yau da yamma, da misalin ƙarfe biyu, an fara taron nuna juyayi, an yi fito, inda dukkanin ma’aikatan sashen daidaita haɗarin jirgin saman MU5735 cikin gaggawa na ƙasar Sin da ma’aikatan ceto da sauran mutanen da abin ya shafa sun tsaya a gaban jirgin saman da ya fadi sun yi shiru har na mintoci 3 domin nuna alhini ga waɗanda suka rasa rayuka yayin haɗarin.

Kana iyalan waɗanda suka rasu, su ma sun nuna alhininsu ƙarƙashin taimakon gwamnatin wurin da ƙungiyar aiki a wurare daban daban.

A halin yanzu, sashen daidaita hadarin cikin gaggawa yana ci gaba da gudanar da bincike kan kayayyakin jirgin saman da gawarwakin waɗanda suka rasu da takardun da abin ya shafa, tare kuma da gudanar da bincike kan musabbabin aukuwar haɗarin.

Fassarawa: Jamila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *