A ranar Ltinin aka rantsar da Janar ɗinda ya jagoranci juyin mulki a ƙasar Gabon, Brice Oligui Nguema, a matsayin shugaban riƙon ƙwarya bayan hamɓarar da Shugaba Bongo.
Janar Nguema, ya jagoranci juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Larabar da ta gabata kan shugaban ƙasar Ali Bongo Ondimba, wanda ya fito daga gidan iyalan da suka mulki ƙasar sama da shekaru hamsin.
Sojoji sun kifar da gwamnatin Bongo ne bayan da aka bayyana na shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a watan da ya gabata bayan da ‘yan adawa suka bayyana zargin cewa an tafka maguɗi.
Jagororin juyin mulkin sun ce sun rusa hukumomin ƙasar, sun soke sakamakon zaɓen, da kuma rufe iyakokin ƙasar, inda daga bisani suka ce sun yanke shawarar buɗe su.
Sai ƙasashen duniya musamman na yankin Afirka ba su amince da Oligui a matsayin halastaccen shugaban ƙasar Gabon ba, wanda yanzu haka ke fuskantar matsin lamba kan ya bayyana shirinsa na maido da mulkin farar hula.
Sabon shugaban gwamnatin mulkin sojin dai ya sha nanata alƙawarin da ya yi na shirya zaɓuka cikin ‘yanci da lumana, ba tare da bayyana lokacin da za a yi ba, amma ya ce sai an fara aiwatar da sabon kundin tsarin mulki ta hanyar ƙuri’ar raba gardama.