An rantsar da sabbin alƙalan Kotun Ma’aikata shida

Daga NASHIR ISAH

A wani mataki na ƙarfafa ɓangaren shari’a na ƙasa, Alƙalin-alƙalai na Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya rantsar da wasu alƙalai sabbin ɗauka su shida na Kotun Ma’aikata.

Rantsarwar ta gudana ne a Kotun Ƙolin da ke Abuja a ranar Litinin.

Yayin rantsarwar, Mai Shari’a Ariwoola ya yi kira ga sabbin alƙalan da su yi aikin da ya rataya a kansu bilhaƙƙi da kuma martabawa daidai da tanadin dokar ƙasa.

Ya ƙara da cewa, ɓangaren shari’ar ƙasar nan na buƙatar maza da mata masu nagarta waɗanda za su kwatanta gaskiya ga ‘yan ƙasa ba tare da tsoro ko tausayi ba.

Ya kuma nusar da alƙalan da su sa ran fuskantar gingima-gingiman shari’o’i masu yawa waɗanda ka iya zuwa tattatare da ƙalubale.

“Ina faɗa muku cewa wajibi ne ku guje wa irin wannan haɗari, mutunci da martabarku abin dubawa ne wanda sai da su za ku samu ɗaukaka a rayuwa,” in ji shi.

Ya kuma faɗakar da su kan cewa in ban da halaka, babu abin da rayuwa da dukiyar da aka cimma ta haramtacciyar hanya ke jefa mutum.

Ya ƙara da cewa, babu wani ma’aikacin shari’a da zai bari a tozarta ɓangaren shari’ar ƙasar nan, yana mai cewa ba zai yiwu a yi wannan tafiya mai dogon zango sannan a ce an gaza ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *