An rantsar da Soludo a matsayin gwamnan Anambara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

An rantsar da Farfesa Chukwuma Soludo da Dakta Onyekachukwu Ibezim a matsayin gwamna da mataimakin gwamnan Anambara a Kudu maso gabashin Nijeriya.
Mai Shari’a Onochie Anyachebelu, Alƙalin Alƙalan jihar ta Anambara, ce ta rantsar da Soludo.

Dukansu sun yi rantsuwar kama aiki da mubaya’a a gidan gwamnatin Anambara a wani biki da ɗaruruwan mutane suka shaida.

A nasa jawabin, Soludo ya ce, sabuwar jihar Anambra da za ta kasance ƙarƙashin jagorancinsa za ta kasance mai bin doka da oda.

Ya godewa gwamna mai barin gado, Cif Willie Obiano da kuma jagororin jam’iyyar APGA bisa gagarumin goyon bayan da suka bayar.

Ya godewa al’ummar Anambara da suka yi masa tambayoyi tare da ba shi aiki ya yi musu hidima a matsayin gwamna.

Soludo ya sanar da dakatar da duk wata tara kuɗaɗen shiga a jihar na tsawon wata ɗaya tare da haramtawa duk wasu kuɗaɗe da gwamnatin Anambara ta biya a wuraren shaƙatawa na motoci, tituna da sauransu.

Ya kuma jaddada buƙatar zaman lafiya tare da yin kira ga matasa da ‘yan siyasa da masu tada zaune tsaye da su rungumi tattaunawa domin wannan shi ne kaɗai maganin zaman lafiya.

An samu cikas na wani ɗan lokaci a wajen bikin sakamakon faɗan da aka yi tsakanin Misis Ebelechukwu Obiano, uwargidan gwamnan mai barin gado da Misis Bianca Ojukwu matar tsohon gwamnan yankin gabas Dim Odumegwu Ojukwu.