An rufe Beijing Olympic 2022: Shin ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu?

Daga AHMAD FAGAM

Bayan shafe sama da makwanni biyu ana fafatawa a gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta ƙasa da ƙasa karo na 24 wanda Beijing ta karɓi bakuncinta a shekarar 2022, za mu iya cewa, da alama kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

An dai buɗe gasar wasannin motsa jikin ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 ne a ranar 4 ga watan Fabrairu, a wani ƙasaitaccen biki wanda ya samu halartar shugabannin ƙasashen duniya da dama da manyan shugabannnin hukumomin ƙasa da ƙasa. Da yammacin ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu, an gudanar da bikin rufe gasar.

Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic ta ƙasa da ƙasa IOC, Thomas Bach, ya bayyana rufe gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing 2022. A jawabin da ya gabatar a wajen bikin rufe gasar, Bach ya bayyana gasar wasannin ta Beijing Olympic 2022 da cewa, “ta musamman ne.” Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa Thomas Bach sun halarci bikin rufe gasar.

Gasar ta Bejing Olmpic 2022 ta samu mahalarta kusan dubu 3 daga ƙasashen duniya da shiyyo kusan 100. Dama dai tun gabanin fara wasannin, shugabanni da dama sun yi gargaɗin cewa gasar Olympic gasa ce ta duk duniya kuma bai kamata a nemi siyasantar da ita ba.

Tun dai a jajiberin rufe gasar yayin cikakken zama na 139 wanda kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa IOC ya shirya a Beijing, shugaban kwamitin Thomas Bach, ya karrama al’ummar ƙasar Sin da kofin Olympics, da nufin gode musu saboda goyon-bayansu ga gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta bana. Bach ya ce, ba don goyon-bayan mutanen Sin ba, da ba za a iya shirya gasar bana tare da samun cikakkiyar nasara ba. Duk da cewa an shirya gasar ta bana a cikin wani yanayi na kulle don hana yaduwar cutar COVID-19, amma Bach ya ji daɗin cikakken goyon-baya daga al’ummar ƙasar Sin. Dama dai masu hikimar magana na cewa, “Fata na gari lamirin.”

Ko shakka babu, gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 ta isar da wani muhimmin sako ga duniya musamman na neman zaman lafiya, da haɗin kan duniya, da sada zumunci, da kawar da kiyayya a tsakanin alummun ƙasa da ƙasa, da neman karfafawa juna gwiwa domin cimma nasarar samar da makoma mai kyau ga dukkan bil adama domin a gudu tare a tsira tare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *