Daga BASHIR ISAH
‘Yan bindiga a Jihar Ribas sun sace ɗan takarar Majalisar Dokokin Jihar yayin da ya rage kwana huɗu kafin zaɓe.
Chukwudi Ogbonna na takarar Majalisar Dokokin jihar ne ƙarƙashin Jam’iyyar Accord, inda yake neman wakilcin al’ummar yankunan Ogba/Egbema/Ndoni da ke jihar.
Bayanai daga yankin sun ce an sace Ogbonna ne ranar Litinin a motarsa a lokacin da yake tuƙi a yankin Rumuigbo da ke kusa da Fatakwal, inda ‘yan bindigar suka tsare shi kana suka yi awon gaba da shi.
Wani ɗan uwan ɗan takarar mai suna Ifeaka Nwakiri, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai a ranar Talata.
A cewarsa, “Sun tafi da shi tare da motarsa ƙirar Marsandi. Mun kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Kala.”
Ya zuwa haɗa wannan labari, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ba ta ce komai kan batun ba.