An sake kwashe ɗalibai a wata makarantar Kaduna

Daga AISHA ASAS

‘Yan bindiga sun sake kwashe ɗalibai a wata makarantar Kaduna da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun a safiyar yau Litinin.

Binciken Manhaja ya gano cewa ‘yan bindigar sun shiga makarantar Bethel Baptist ne da sanyin safiyar Litinin inda suka yi ta harbin bindiga a sama sannan suka kwashi na kwasa daga cikin ɗalibai.

Bayanai daga yankin sun nuna wasu mutum biyu sun rasu sakamakon harin, kuma wasu daga cikin ɗaliban sun samu zarafi sun tsere daga hannun barayin.

Wannan shi ne karo na huɗu a tsakanin watanni shida da suka gabata inda ‘yan bindigar ke shiga Kaduna suna wawushe ɗalibai.

Ya zuwa haɗa wannan labari babu wani bayani a hukumance da ya tabbatar da harin, haka nan ba a kai ga tantance adadin ɗaliban da ‘yan bindigar suka kwashe ba.

Ko a jiya Lahadi, sai da wasu ‘yan bindiga suka farmaki Cibiyar Kula da Tarin Fuka da Kuturta ta Ƙasa da ke Zaria inda suka yi garkuwa da mutum sama da bakwai, ciki har da wata mai shayarwa.