An sake yin nasarar bada darasi daga cibiyar binciken sararin samaniyar ƙasar Sin

Da CMG HAUSA

Jiya ne, aka gudanar da aikin ba da darasi karo na biyu daga cibiyar binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin wato Tiangong, inda ‘yan sama jannati guda uku da suka haɗa Zhai Zhigang da Wang Yaping da kuma Ye Guangfu suka koyawa yara ilimin kimiyya dake shafar ayyukan sararin samaniya, inda suka nuna wa yara wasu na’urorin nazari da yanayin da suke rayuwa a cibiyar.

Darektan cibiyar raya fasahohin sararin samaniya ta cibiyar kimiyya ta kasar Sin Zhang Wei ya fayyace cewa, nan gaba za a ci gaba da gudanar da aikin ba da darasi a cibiyar binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin ta hanyoyi daban daban, yana mai cewa,

“Hakika mun fi mai da hankali kan sha’awar da ɗaliban makarantar midil da ta firamare suke da ita kan ilmin kimiyya, ta yadda matasan ƙasar Sin za su shiga aikin nazarin kimiyya a nan gaba, saboda muna ganin cewa, idan ƙasa tana son samun ci gaba, dole ne ta ƙara haɓaka aikin nazarin kimiyya, don haka akwai buƙatar matasa su ƙara shiga aikin.”

Fassarawa: Jamila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *