An sake zaɓar Motsepe a matsayin shugaban CAF

Daga BELLO A. BABAJI

Shahararren Attajiri daga ƙasar Afirka ta Kudu, Patrice Motsepe ya sake zama Shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), biyo bayan sake zaɓan sa da aka yi ba tare da abokin karawa ba.

A shekarar 2021 ne aka zaɓe Motsepe mai shekaru 63 a matsayin shugaban CAF, inda ya sake jaddada aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar a watan Oktoban 2024.

An tabbatar da shugabancin nasa ne a babban taron CAF da aka gudanar a birnin Cairo a ƙasar Misira, wanda ya samu halartar shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Ƙasa-da-ƙasa (FIFA), Gianni Infantino, ranar Laraba.

Baya ga zaɓen Motsepe wanda zai sake jan ragamar shugabancin ma shekara huɗu ne aka kuma gudanar da zaɓen mambobin majalisar zartarwar hukumar, inda tsohon ɗan wasan Kamaru, Samuel Eto’o ya samu kujera.

Haka kuma an zaɓi wakilan Nahiyar Afirka a majalisar FIFA yayin taron.