An sake zaɓe a ƙananan hukumomi 16 a Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

A ranar Asabar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta sake zaɓe a wasu ƙannan hukumomi guda 16 a Jihar Kano.

Ƙananan hukumomin Fagge da Ungoggo da Dawakin Tofa da Makoɗa, Warawa da sauran na daga cikin wuraren da sake zaɓe ya shafa.

Mahaja ta kalato cewar tun da misalin ƙarfe 7:30 na safe da yawan masu zaɓe sun fito domin kaɗa ƙuri’arsu.

Sauran yankun da zaɓen ya shafa har da Gabasawa, Gezawa, Tudun Wada, Doguwa, Gwarzo, Takai, Garko, Wudil, Ajingi, Danbatta da kuma Gaya.

Wasu masu sanya ido kan zaɓe sun bayyana wa Manhaja gamsuwarsa dangane da yadda jama’a suka fito zaɓe da kuma isowar kayan zaɓe a kan kari.

Hadiza Bala, ɗaya daga cikin masu sa ido a harkar zaɓen, ta ce wannan karon masu zaɓe sun fito da yawa fiye da lokacin baya.

“Kamar yadda kuke gani yanzu haka an samu masu kaɗa ƙuri’a da yawa sun fito, haka kuma na’urar BVAS na aiki muna gani babu wata natsala.

“Na’urar BVAS na tantance masu kaɗa ƙuri’a cikin lokaci, fatan a samu gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali,” in ji ta.

Bashir Anwar wanda mazaunin Fagge ne, ya ce wannan zaɓe jama’a sun fito da yawa, kuma an girke jami’an tsaro da dama gurin da yawan sannan zaɓe na gudana cikin lumana.

“Ina ganin za a samu nasara mai yawa tare da aiki nagari,” in ji shi.