An samu haɗarin tankar mai a Legas

Daga WAKILINMU

Haɗarin ya auku ne a ranar Alhamis a yankin Cocin MFM da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Bayanai sun tabbatar cewa an samu hasarar rayuka sakamakon haɗarin wanda ba a kai ga tantance adadinsu ba.

Ko a Larabar da ta gaba an samun makamancin wannan haɗarin a Legas inda gobara ta tashi ta laƙume wani gidan mai a daidai lokacin da ake sauke mai daga tankar mai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *