An samu karin mutane 550 dauke da cutar Korona a Najeriya

An samu karin mutane 550 dauke da cutar Korona a Najeriya. Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa ce ta bayyana hakan a shafinta na intanet.

Shafin dai ya bayyana cewa, karin da aka samu, ya sanya alkaluman masu dauke da cutar ya kai addadin mutum 70,195.

Haka kuma hukumar ta bayyana  cewa an samu karin wadanda suka mutu, wanda a yanzu cutar ta halaka yawan mutane da ya kai  1,182. An samu wannan karin masu dauke da cutar ne daga jihohi 16 da suka hada da babban birnin tarayya Abuja.

Jihar Legas dai ita ke kan gaba har yanzu da mutum 219, sai jihar Kaduna 56, kwara 19, Kano 15, Rivers 15, Sokoto 10, Enugu 9, Gombe 8, Plateau 7, Osun 7, Anambra 5, Oyo 5, Jigawa 4, Ogun 4, Bauchi 2, Edo 1, sai kuma babban birnin tarayya Abuja 168.

Sai dai jawabin ya ce, a yanzu haka an sallami mutum 163 da suka samu sauki a duk fadin kasar nan.

Kamfanin dillacin labarai na Nigeria ya bayyana cewa, wannan alkaluma da hukumar ta fitar, shi ne mafi yawa da aka taba samu a kasar, tun bayan na 23 ga watan Ogusta.

Hukumar ta yi bayanin cewa, a halin yanzu dai sama da mutum 60,000 ne suka warke, yayin da kuma sama da mutum 1000 suka rasu a sakamakon cutar a duk fadin kasar nan.

Hukumar ta yi kira ga yan Najeriya da su dage wurin daukar matakan da za su dakile yaduwar cutar, musamman a lokacin bukukuwan kirsimeti. Ta hanyar kaurace wa kasashen da cutar ta yi kamari, da kuma nisanta da juna a yayin taruka.

A yanzu haka dai hukumar ta ce ta yi wa sama da mutune 800,00 gwajin wannan cuta a duk fadin kasar nan, tun daga 27 ga watan Fabrairu na wannan shekarar.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*