An samu rarrabuwar kawuna a Majalisar Dattawa game da hukuncin kotu kan Dokar Zaɓe

Daga WAKILINMU

An samu rarrabuwar kawuna yayin zaman sanatoci a wannan Talatar dangane da kiran da aka yi wa Majalisar Dattawa na tafka muhawara kan hukuncin da Babbar Kotu ta yanke game da haramta Sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe.

Rikicin ya soma ne sa’ilin da Sanata George Sekibo daga jihar Rivers, ya dogara da doka ta 10 da ta 11 na dokokin majalisa wajen nusar da takwarorinsa irin ayyukan da suka rataya a kan sassa ukun da gwamnati ke da su, wato ƙananan hukumomi, jihohi da kuma gwamnati tarayya.

Ya ce hukuncin da kotun ta yanke na sauke matakin da majalisar ta ɗauka mummunan al’amari ne da bai kamata a bar shi haka ba.

Yana ƙara da cewa idan har aka bar batun, to fa jam’iyyun siyasa za su iya ƙalubalantar matsayoyin majalisar a gaban kotuna.

Daga nan Sanata Sekibo ya buƙaci takwarorinsa da su dakatar da sauran ayyukan majalisar na ranan domin zama tare da tafka muhawara kan batun.

A cewar Sanata Sekibo, “Wannan batu yana da matuƙar muhimmanci. Waɗanda suka je kotu don ƙalubalantar matakinmu ba su haɗa da mu a matsayin waɗanda ke da sha’awar kan batun ba. Ba mu ma san cewa wani lamari na gaban kotu ba. Ba zato ba tsammani, sai aka ce mana an yanke hukunci, nan take Gwamnatin Tarayya ta ɗauke shi.

“Hakan na da haɗari kuma muna buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Wannan na da muhimmanci don daidaita irin waɗannan abubuwan.”

Daga bisani, majalisar ta ɗage muhawarar kan lamarin zuwa gobe Laraba bayan jin ra’ayoyi mabanbanta kan wannan batu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *