An samu wasu yan takara da alamun shan kwaya a Kano

Shugaban hukumar yaki da shan kwaya ta kasa mai kula da shiyyar Kano, ya bayyanawa manema labarai, an samu wasu daga cikin yan takarar zama shugabannin kananan hukumomin jihar Kano da wasu alamu da ke nuna, kodai sun taba shan kwaya, ko kuma suna sha.

Wannan bayani ya biyo bayan tantance yan takarar ne da hukumar ta yi. In an tuna gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa dokar hana kowa tsayawa takara, ko rike wani mukami a jihar,  har sai an tabbatar da ba ya shan kwaya.

A yayin da ya ke jawabi ga manema labarai, kwamandan rundunar hana shan kwayar, Dafta Ibrahim Abdul, ya bayyana cewa hukumar sa ta tantance yan takarar da za su tsaya a zaben da za a gudanar a watan Fabrairu na shekara mai zuwa, har mutum 250, kuma an samu wasu daga cikin su, da alamun shan kwaya ba bisa ka’ida ba.

Ya kara da cewa “Gwamnatin jihar Kano kan aiko mana da sunayen mutane da za mu tantance, kama daga kwamishinoni, adbeza da wadanda za a nada a mukamin hakimci, kuma mu kan tantance su. Saboda dokar jihar Kano ta hana yan kwaya tsayawa takara, ko rike wani mukami”

A yanzu dai an tantance sama da yan takara 250 masu neman tsayawa takara a zaben mai zuwa, kama daga chiyamomi zuwa kansiloli, daga kananan hukumomi 19.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*