An sauke tsoffin shugabannin ƙungiyar yaɗa manufar Buhari ta ƙasa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

An sauke tsoffin shugabannin ƙungiyar yaɗa manufar Buhari daga ƙaragar jagorancin ƙungiyar ta ƙasa wato Buhari Campaign Organization (BCO). 

An sauke su ne saboda zargin yi wa mabiya ‘ya’yan ƙungiyar rashin adalci tare da ƙoƙarin azurta kansu ta hanyar nema wa kansu kwangila mai tsoka a ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban.

Sakamakon haka ne ya sa ‘ya’yan ƙungiyar a ɗaukacin jihohi 36 suka yi wani taron gaggawa a jihar Jigawa a makon da ya gabata a ƙarƙashin jagorancin Tukur Sambo suka bada sanarwar tunɓuke su daga kan kujerunsu, kuma suka zaɓi sabbin shugabannin da suke da yaƙinin za su yi wa kowa adalci.
 
A yayin zaɓen sun maye gurbin shugaban da Tukur Sambo a matsayin sabon shugaban  da zai jagoranci ƙungiyar a matakin ƙasa.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin sabon shugaban da ya amshi ragamar mulkin ƙungiyar Malam Tukur Sambo wanda ya raba wa manema labarai takaddar bayan taro jim kaɗan bayan kammala taron su a ɗakin taro na ƙungiyar malamai ta ƙasa reshen jihar Jigawa.

Tukur Sambo ya zargi tsoffin shugabannin ƙungiyar da rashin adalci ga ‘ya’yan ƙungiyar musamman waɗanda suke can ƙasa-ƙasa ba a yin komai dansu saboda abin da ya kira da rashin adalci.

Ya ƙara da cewa an yi watsi da ‘ya’yan ƙungiyar, ba a yin komai da su iyakacin tsoffin shugabannin ƙungiyar ne kawai suke damawa babu wani da yake amfana daga romon dimukuraɗiyya sun tura mota an bar su da hayaƙi; gwamnati tana ganin jama’ar da suka yi mata wahala suna amfana, amma su kaɗai ne suke kwana akan abinda ake bayarwa domin amfanin ‘ya’yan ƙungiyar.

Ya ce sun ɗauki matakin sauke su ne domin dawo da martabar ƙungiyar a idon duniya bayan ɓata wa ƙungiyar suna da tsoffin ‘ya’yanta suka yi ba don komai ba kowa ya san Maigirma Shugaban Ƙasa Buhari ya yi rawar gani kuma ba zai sake tsayawa takara ba. Don haka ba za su bari wasu mutane suna amfani da sunan ƙungiyar suna yin abinda suka ga dama ba.

Sabon shugaban ya yi alƙawarin ceto ƙungiyar tare da dawo da martabarta a idon duniya. Musamman wajen cika alƙawuran da jam’iyyar APC ta ɗauka wa ‘ya’yan ƙungiyar a lokacin yaƙin neman zaɓe musamman a wannan ƙoƙari da sabon shugaban yake yi na gyara jam’iyyar wato maigirma gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni don ganin an dawo da martabar jam’iyyar kafin sabon zaɓe da za a shiga nan gaba kaɗan.