An sauke wa acaɓa, keke napep farashin fetur zuwa N430 a Borno

An sauke farashin litar mai zuwa Naira 430 don amfanin ‘yan acaɓa da matuƙa adaidaita-sahu da ‘yan taksi a jihar Borno.

Bayanai sun ce ƙaddamar da dogayen motoci guda 70 da gwamnatin jihar ta yi don rage raɗaɗin rayuwa inda jama’a kan biya N50, hakan ya sa sauran masu abubuwa na ‘yan kasuwa a jihar kowa na neman matsaya.

An ce wasu masu hannu da shuni a jihar suka bai wa gidajen mai a babban birnin jihar kwangilar sayar da fetur N430 kan kowace lita a maimakon N637.

Bayanai sun ce masu hannu da shunin sun ɗauki wannan mataki ne a matsayin tasu gudunmawa game da ba da tallafin rage raɗaɗin cire tallafin fetur da ‘yan ƙasa ke fuskanta.

Ibrahim Jibrin Mohammed, na daga cikin masu kula gidajen mai a jihar, ya bayyana cewa ya yaba da yadda Uwargidan Shugaban Ƙasa, Mrs Oluremi Tinubu, take takan tallafa wa mabuƙata da waɗanda iftila’i ya same su a sassan ƙasa.

Wani mai sana’ar tuƙa Keke NAPEP a jihar, Yakub Bukar, wanda shi ma ya ci moriyar tallafin, ya ce tallafin ya zo a daidai lokacin da ake da buƙatarsa inda ‘yan jihar ke wayyo-wayyo da raɗaɗin cire tallafin mai.