An shawarci al’ummar Kano su guji haifar da tashin-tashina kafin da bayan zaɓe

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Zaɓaɓɓen Sanatan shiyyar Kano ta Kudu, Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyarsa ta NNPP da ke jihar da su rungumi zaman lafiya a yayin zaɓe da bayan zaɓe musamman a Ƙaramar Hukumar Rogo da ke jihar.

Wannan na cikin wata takarda da kakakin Sanatan, Ashiru Shehu Kachako, ya miƙa wa Blueprint Manhaja a Kano,

Sanatan ya yi jawabin ne a yayin da ya kai ziyara nuna jin daɗinsa da godiya ga al’ummar shiyyar Kano ta kudu dangane da zaɓen shi suka yi a zaɓen da ya gabata.

Ya ce babu wata al’umma da za ta kai ga nasara a rayuwa sai ta yi haƙuri a rayuwa.

“A tafiyarmu, ba mu yarda da ta’addanci ba, kuma ina sake kira ga jama’armu da su fito mu zaɓi jam’iyyarmu ta NNPP cikin hikima da lumana”.

Kazalika, ya yi kira ga al’umma da su zaɓi Abba Kabir Yusif a matsayin gwamna da ‘yan majalisar dokokin Jihar Kano a ƙarƙashin NNPP.