An shawarci al’ummar Musulmi su ɗauki matakin kariya daga zafin rana saboda azumi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugabar Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Unguwar Zoma ta Jihar Kano, Hajiya Mairo Sa’id Muhammad ta sharwarci al’umma akan ɗaukar matakan kariya akan yanayin tsananin zafi da ake fuskanta musamman a cikin watan Ramadan ɗin nan.

Ta ce bisa yadda ake samun zafi da ƙwallewar rana a wannan lokaci ya kamata Musulmi su riƙa ɗaukar matakan samun sauƙi wajen gudanar da ibadunsu, musamman ta guje wa shiga rana, saboda tsananin zafi, sannan a lokacin buɗa baki a kauce wa soma amfani da ruwa mai sanyi. Ta ƙara da ce an fi buƙatar a samu ruwa mai ɗan ɗumi da zai warware hanji.

Hajiya Mairo Sa’idu Muhammad ta sharwarci al’umma wajen kula da tsaftar kayayyakin abinci da na marmari da suke ta’ammali da su damin samun ingantacciyar lafiya.

Sannan ta bayyana muhimmancin amfani da cin dabino ga mai azumi kasancewar yana da sinadarai da yawa da suke da amfani ga jikin ɗan Adam. Kazalika kuma a taƙaita wajen amfani da maiƙo.

Shugabar kwalejin ta ja hankalin ma’aikatan jinya da malamai dake koyon sanin makamar aiki a asibitoci akan rivanya ƙoƙari wajen kula da marasa lafiya da yin haƙuri da su; don a ɗabi’arsu ta aikin jinya akwai haquri da marasa lafiya da kwantar musu da hankali.