Daga DAUDA USMAN a Legas
An shawarci al’ummar Musulmin Nijeriya musamman maniyyata aikin Hajjin bana da su zama jakadu nagari yayin gudanar da aikin Hajji a ƙasa maitsarki.
Sarkin Fawan Ƙaramar Hukumar Amuwo Odofin dake cikin garin Legas, Alhaji Usaini Iliyasu shi ne ya yi wannan kiran yayin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke cikin kasuwar Amuwo Odofin, sa’ilin da yake yin sallama da wasu mahauta masu niyyar tafiya aikin Hajjin bana.
Usaini ya cigaba da cewa a sakamakon waɗansu maniyyata ‘yan Nijeriya suna haɗa gudu da susar katara wajen zuwa ƙasa mai tsarki domin su sauke farali, suna sayen haramtattun kaya waɗanda gwamnatin Saudiyya ta haramta shig da su cikin ƙasarta, suna saye suna zuwa da shi, wanda a cewarsa hakan ba daidai ba ne, tunda idan aka kama mutum ya ɓata aikin da ya kai shi ƙasa maitsarki.
Sarkin Fawan ya kuma yi kira ga maniyyatan da su saka ƙasarsu Nijeriya cikin addu’o’i yayin gudanar da ibadunsu a harami, inda ya ce maniyyatan su roqa wa Nijeriya damuwar da take ciki na matsalolin ta’addanci da garkuwa da mutane da sauran ƙalubalen da ke addabar ƙasar.
A ƙarshe ya yi wa maniyyatan fatan Allah Ya sa su gudanar da ibadunsu lafiya kuma karɓaɓɓiyar ibada.