An shirya gudanar da babban taron KILAF na bana

Daga BASHIR ISAH

Kamfanin Moving Image Limited tare da haɗin gwiwar Tsangayar Nazarin Sadarwa ta Jami’ar Bayero, Kano, sun shirya gudanar da babban taronsu na shekara-shekara na tallata harsunan gida na Kano a kasuwar fina-finai ta Afirka, wato Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival ko kuma KILAF a taƙaice.

Taron KILAF na 2021 zai gudana ne a ranakun Litinin 22 da Talata 23 ga watan Nuwamban da ake ciki. Wannan shi ne karo na huɗu da ake shirya taron.

Sanarwar manema labarai da ta sami sa hannun mu’assasin KILAF, Abdulkareem Mohammed da shugaban tsangayar nazarin sadarwa na jami’ar Bayero, Kano, Farfesa Mustapha N. Mallam ta nuna kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Moving Image Limited da Tsangayar Nazarin Sadarwa ta Jami’ar Bayero, Kano, wajen tallata KILAF.

Haka nan, sanarwar ta ce za a halarci taron ne ta hanyar zuwa a zahiri da kuma ta intanet tare da cikakken kiyaye dokokin korona.

Ta ci gaba da cewa, ga waɗanda za su halarci taron a zahiri, wurin taron shi ne Tsangayar Nazarin Rawa da Wasanni na Jami’ar Bayero da ke sabon wuri na jami’ar. Sannan ga waɗanda za su halarta ta intanet, akwai buƙatar su yi rijista kafin taron ta hanyar amfani da adireshi: https//kilaf.movingimage.africa/register.php. Tare da cewa, taron zai gudana ne daga ƙarfe 9 na safe zuwa 5 na yamma na kowace rana.

A cewar sanarwar, KILAF wata muhimmiyar hanya ce ta yauƙaƙa dangantaka tsakanin ‘yan fim da masana da ‘yan jarida da sauransu a sassan Afirka baki ɗaya.

Masu shirya taron sun hararo cewa, lallai ne ana fuskantar ƙalubalai iri-iri a faɗin duniya da suka haifar da cikas ga harkokin shirya fina-finai da sauransu sakamakon annobar korona. Sun ce, duk da wannan akwai damarmaki ga masu shirya fina-finai na Afirka inda za su yunƙura don samar da mafita ta hanyar amfani da fasaha wajen ƙirƙiro da sababbin hanyoyi kasuwanci.

Taken taron na bana zai maida hankali ne kan abin da ya shafi samun daidaito kan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga bayan lafawar guguwar annobar korona.

Haka nan, yayin taron ana sa ran gabatar da muƙalu daban-daban da tattaunawa kan muhimman batutuwa da kuma tambayoyi da amsoshi masu alaƙa da taken taron.