An shirya tattaunawa tsakanin shugabannin matasan Sin da Afirka karo na biyu ta kafar bidiyo

Daga CMG HAUSA

Da yammacin jiya Jumma’a ne, ƙungiyar sada zumunta tsakanin Sin da kasashen ƙetare ta al’ummar ƙasar Sin, ta shirya taron tattaunawa tsakanin shugabannin matasan Sin da Afirka mai taken “Amfani da kuzarin matasa domin samar da kyakkyawar makomar bil Adama” karo na biyu ta kafar bidiyo, inda wakilan ƙungiyar sada zumunta tsakanin Sin da Afirka da wakilan matasan da suka zo daga ƙasar Sin da ƙasashen Afirka 35 suka halarci taron.

Yayin taron na jiya, matasan Sin da Afirka sun yi musanyar ra’ayoyi mai zurfi kan batutuwan da suka haɗa da “Hangen matasa: Muhimman al’adun da ake buƙata yayin gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai ɗaya”, da “Burin matasa: Ma’anar
zamanintarwa irin na ƙasar Sin ga duniya”, “Aikin matasa: Managartan matakan da za a ɗauka domin tabbatar da muradun raya duniya” da sauransu.

Jakadan ƙasar Senegal dake ƙasar Sin brahima Sory Sylla ya yaba da sakamakon da ƙasar Sin ta samu wajen kawar da talauci, ya bayyana cewa, makomar duniya tana hannun matasa ne, don haka ya dace a samar da damammaki ga matasa domin su gina makomar duniya mai haske.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa