An soma bincike kan haɗarin jirgin da ya ci ran Attahiru a Kaduna – Cibiya

Daga AISHA ASAS

Cibiyar Binciken Haɗurra a Nijeriya (AIB-N) ta soma gudanar da bincike kan haɗarin jirgin saman da ya auku a Kaduna a Juma’ar da ta gabata wanda ya yi sanadiyar mutuwar Babban Hafsan Hafsoshi, Ibrahim Attahiru tare da wasu jami’ai.

Babban Manajan Sashen Hulɗa da Jama’a na Cibiyar, Tunji Oketunbi, shi ne ya bayyana hakan a wani bayani da ya fitar a Legas a Asabar da ta gabata.

Oketunbi ya ce tuni cibiyar ta sunkuya bincike don gano musabbabin aukuwar haɗarin wanda a cewarsa har ma an kai ga gano wasu muhimman na’urori a inda jirgin ya rikito wanda za su taimaka wajen gudanar da  binciken.

Ya ce “Masu binciken za su sauke muryoyin da ke cikin na’urar naɗar magana da aka gano don zurfafa bincike a ɗakin biniciken cibiyar da ke Abuja.

“Nauyin da aka ɗora wa AIB-N na yin binciken ya daidata ne da Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MOU) da aka rattaba wa hannu a tsakanin hukumomin biyu a ranar 1 ga Yuli, 2020 wanda ya shafi tallafa wa juna a inda buƙatar hakan ta taso,” in ji Oketunbi.

Kazalika, ya ce ana sa ran gudanar da sahihin bincike kuma a ƙarƙashin kulawar ƙwararrun jami’ai.

A

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *