Atsi Kefas, ƙanwar Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas ta rasu bayan harbin ta da aka yi daga ɗaya daga cikin ƴan sanda masu tsaron lafiyarta yayin da suke ƙoƙarin kare ta daga harin ƴan bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa ta rasu ne a wani asibiti da ke Abuja, inda aka kai ta don samun kulawa.
Wani majiyarmu ya bayyana cewa, “Ta rasu daren jiya sabida raunuka da ta samu. Har yanzu gwamna da iyalansa ba su fitar da wata sanarwa kan rasuwar Atsi Kefas ba.
Muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalan gwamnan a wannan lokaci.”
Wata majiya ta ƙara tabbatar da lamarin, tana cewa, “Haƙiƙa ƙanwar Gwamnan Jihar Taraba, wadda ƴan bindiga suka harba yayin tafiyarta zuwa Abuja, ta rasu.”
A halin yanzu, gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da wannan mummunan lamari da ya faru.