An tantance mutum miliyan ɗaya don yin aikin ƙidaya — NPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamishinar Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) mai wakiltar Jihar Benuwai, Patricia Kupchi, ta ce kimanin ma’aikata miliyan ɗaya aka tantance domin yin aikin ƙidayar 2023.

An ɗage ƙidayar, wadda aka shirya yi a watan Mayu, sai dai har yanzu ba a bayyana ranar da za a yi ba.

Kupchi, a jawabinta da ta gabatar a wajen wani taro kan yadda aka sake tsara ƙidayar yawan jama’a da gidaje na 2023 a Makurdi, ta ce hukumar za ta ci gaba da wayar da kan jama’a har sai an sanar da sabuwar ranar yin ƙidayar.

“An kammala ɗaukar ma’aikatan wucin gadi ne kafin sake jadawalin ƙidayar jama’a ta hanyar tsauraran matakai ta intanet, inda aka tantance ma’aikata kimanin miliyan ɗaya aka kuma gano cewa sun cancanci yin aikin.

“Hukumar ta samu mataimaka na musamman don kidayar 2023. Kimanin na’urori 500,000 aka kai ofisoshin da ke jahohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja domin yin aikin da su,” inji ta.

Kupchi ta ce dage jadawalin ya bai wa hukumar damar qara inganta matakai da tsare-tsare don gudanar da ƙidayar jama’ar yadda ya kamata.

Ta bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin ƙidayar 2023 za ta zamo mafi alfanu ga kowa.