An taskace ‘yan Nijeriya miliyan 30 a Rajistar Al’umma ta Ƙasa, inji Minista

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ta ce ta rubuta sunayen mutane da ba za su gaza miliyan 30 ba a Rajistar Al’umma ta Ƙasa (National Social Rajista, NSR) wadda za a yi amfani da ita a samu sauƙin ceto mutane miliyan 100 daga fatara a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a taron Sakatarorin Dindindin na jihohi kan shirin gwamnati na magance matsalolin yau da kullum (National Social Safety Nets Project, NASSP), wanda aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja.

Ministar ta samu wakilcin Sakataren Dindindin a ma’aikatar, Alhaji Bashir Alƙali, a taron.

Ta ce aikin da aka ɗora wa ma’aikatar na gudanar da shirin na NASSP tare da tallafin Bankin Duniya, ana yin shi ne domin a rage fatara da matsalolin yau da kullum a Nijeriya.

Hajiya Sadiya ta ce an tsara shirin na NASSP ne domin ya kasance ya na da ofisoshi daga matakan tarayya zuwa jihohi, har zuwa yankunan ƙananan hukumomi, wato ya nuna matakai uku na gwamnati.

Ta ce, “A yanzu, rajistar NSR ta na da sunayen ‘yan Nijeriya miliyan 30 daga jihohi 36 da Yankin Babban Birnin Tarayya daga gidajen matalauta guda miliyan bakwai.

“Idan an ƙara lissafawa, za a ga cewa an samo waɗannan gidajen ne ya zuwa yanzu a yankunan ƙananan hukumomi 699, mazaɓu 8,161 da al’ummomi 81,776 a sassan ƙasar nan.

“An samar da rajistar ta NSR ne ta hanyar yin amfani da tsarin fasalin ƙasa da al’umma, ta hanyar amfani da jama’ar unguwa, wanda ofishin kula da tsarin a jiha (SOCU) ya ke tattarawa a kowace jiha.

“Ofishin raba kuɗi na ƙasa (National Cash Transfer Office, NCTO), a yanzu ya samu gidajen matalauta da ke amfana da shirin guda 1,632,535 a al’ummomi 45,744 daga unguwanni 5,483 na yankunan ƙananan hukumomi 557 da ke jihohi 35 da yankin Abuja.”

A cewar Sadiya, wannan na nuna cewa an samu mutum 8,100,682 a gidajen da ke cin moriyar shirin ta hanyar wakilin kowane gida wanda ake kira ‘Caregiver’ ko ‘Alternate Caregiver’ wanda ake biya sau biyu a wata (N10,000).

Ta ƙara da cewa a yanzu, gidaje 991,965 ne su ke karɓar kuɗi a jihohi 28 da yankin Abuja.

Ta nanata cewa dukkan waɗannan abubuwa an yi su ne da nufin cika burin Shugaba Muhammadu Buhari na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga matsananciyar fatara.

Ta ce, “Don haka, akwai buƙatar a daidaita ofisoshin shirin na SOCU da yadda ake gudanar da shi. Hakan na da matuƙar muhimmanci.”

A nasa jawabin, Babban Kodineta na NASSCO, Mista Apera Iorwa, ya ce manyan sakatorin shirin a jihohi su ne ma’aikata masu sanya ido kan shirin a jihohin su.

Ya ce, “Akwai buƙata a gare mu da mu riƙa haɗuwa a kai a kai domin mu yi nazarin al’amura da tsare-tsare tare da gano hanyar da za a samu cigaban shirin.”

Mista Iorwa ya ce tilas ne manyan sakatorin su tashi tsaye domin su tabbatar ba a kautar da manufar shirin a jihohin su ba.

Ya ce an tsara cewa jihohi za su mayar da kuɗin ga Bankin Duniya domin za a yi binciken kowane asusu kuma idan aka gano cewa kuɗi sun salwanta, to tilas ne a dawo da su a biya.

Haka shi ma Kodinetan Shirin Tiransifar Tsabar Kuɗi na Ƙasa (Conditional Cash Transfer), Ibrahim Jafar, ya ce tafiya tare da dukkan masu ruwa da tsaki a shirin ya na da muhimmanci ga samun nasarar shirin.

Ya ce akwai matuƙar muhimmanci a san bambancin da ke akwai tsakanin Rajistar Masu Cin Moriya ta Ƙasa (National Beneficiary Register) da Rajistar Al’umma ta Ƙasa (National Social Register).

Ya bayyana cewa akwai wasu matsaloli da ake samu wajen biyan kuɗi, to amma nan ba da daɗewa ba za a warware yawancin su.

Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa a yayin da wasu Sakatarorin Dindindin su ke gode wa Ma’aikatar Harkokin Jinƙai saboda wannan damar da aka samu, wasu kuwa sun koka kan babbar tazarar da aka samu tsakanin su da SOCU saboda NASSCO.

A lokacin da ya ke magana kan hakan, Mista Iorwa ya nanata cewa daga yanzu za a fara magance matsalar, kuma duk wani bayani da aka miƙa wa SOCU to za a miƙa shi ga su Sakatarorin Dindindin ɗin.