An tsare tsohuwar matar MKO Abiola a kurkuku bisa zargin cin mutuncin ‘yar sanda

Daga WAKILINMU

An ingiza ƙeyar tsohuwar matar shahararren ɗan kasuwa kuma ɗan siyasar nan, MKO Abiola, Zainab Duke-Abiola, ya zuwa gidan kaso a garin Suleja bisa zargin cin mutuncin ‘yar sandan da ke ba ta kariya, Teju Moses.

Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani ya nuna yadda Zainab wadda lauya ce kuma ‘yar gwagwarmayar kare ‘yancin bil Adama, ta umarci ‘yar aikinta, Rebecca Enechido, kan ta duki Teju saboda ƙin yin wasu ayyuka da ta ɗora mata.

An ga jami’ar cikin rigar aiki yayin da jini ke fita daga jikinta zaune dirshan a ƙasa tana neman a ɗauke ta zuwa asibiti don yi mata magani.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis da ta gabata, Mai Magana da Yawun ‘Yan Sanda, CSP Muyiwa Adejobi, ya tabbatar da an kama Farfesa Zainab tare da ‘yar aikinta Rebecca Enechido.

Sanarwar ta ce, wadda ake zargin ta aikata laifin da ake tuhumar ta da shi ne a ranar Talata, 20 ga Satumba, 2022, tare da taimakon ‘ya aikinta Rebecca Enechido a gidanta da ke yankin Garki, Abuja.