An tsinci ƙwarangwal ɗin magidanci kan gadon ɗakinsa bayan shekaru huɗu ana nemansa

Daga WAKILINMU

Mutane a shafukan sada zumunta sun shiga zullumi tun bayan da aka samu ƙwarangwal ɗin wani mutum a cikin ɗakinsa, bayan shekaru huɗu da rasuwarsa a garin Apete da ke birnin Ibadan na Jihar Oyo.

Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Oyo ta tabbatar da samun gawar magidancin da aka shafe shekaru huɗu ana nemansa.

Rundunar ‘Yan Sandan ta ce, hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (CID) ta fara gudanar da binciken gawar wani aka gano a cikin ɗakin kwanansa da ke yankin Awotan, unguwar Apete a Ibadan.

Ana tunanin cewa, kwarangwal ɗin gawar wanda ba a bayyana ba, an samu rahoton ta ne daga makwabta shekaru huɗu da suka wuce a yayin da ya ke zuwa daga Ibadan zuwa Fatakwal a garin Kuros Ribas, inda a nan ya ke zaune a wancan lokacin.

Wasu masu aikin gayya a Unguwar Awotan ne suka tsinci gawar mamacin bayan da suka nemi izinin ’yan sanda domin su kutsa kai cikin gidansa su sare ciyayun da suka tsiro a harabar gidan da ya shafe shekaru a rufe.

Yayin da suke aikin ne suka lura an buɗe taga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, wanda hakan ya sa suka leƙa cikinsa, sai suka gano gawar mamacin manne akan gadonsa yana kwance.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya tattaro daga mazauna yankin cewa an ga marigayin ne shekaru huɗu da suka gabata.

Haka zalika, marigayi Abiola ya kan zo Ibadan lokaci-lokaci daga Abuja kuma ba shi da wata alaƙa mai ƙarfi da makwabtansa.

Da ya ke tsokaci a kan lamarin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Oyo, SP Adewale Osifeso, ya ce, kwamishinan ’yan sandan jihar, Adebowale William, ya tura wata tawagar masu binciken laifuka zuwa gidan mamacin.

SP Osifeso ya ce, kwamishinan ’yan sandan ya kuma bayar da umarnin miƙa lamarin ga hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (SCID), domin gano musabbabin mutuwarsa.

Kakakin ’yan sandan ya ce, ’yan uwan marigayin sun tabbatar da rabon da su ga marigayin tun shekarar 2018, shekaru huɗu da suka wuce.

A cewar Osifeso, kwamishinan ’yan sandan ya yi kira ga jama’a masu kishin ƙasa da su taimaka wajen samar da bayanai masu amfani domin warware zare da abawa.

Ya kuma bada tabbacin da zarar sun kammala bincike za su bayar da cikakkun bayanai ga jama’a.