An tsinci gawar ɗaliba cikin rami bayan vatarta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An tsinci gawar wata ɗalibar Jami’ar Tarayya ta Oye Ekiti (FUOYE), Atanda Modupe Deborah, kwanaki biyu bayan ta ɓata.

A cewar rahotanni, Deborah, wacce ɗaliba ce a sashen karatun aikin jinya, stream A, Faculty of Basic Medical Science, ta ɓata bayan ta tafi karatun daren Litinin, 4 ga Satumba, 2023.

Abokan zamanta sun bayyana ɓatarta lokacin da ba ta dawo daga karatun dare ba.

An tsinci gawar ta binne a wani rami mara zurfi a bayan jami’ar ba tare da idanunta ba a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Da ya ke mayar da martani kan lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Laraba, magatakardar jami’ar, Mufutau Ibrahim, ya umarci dukkan ɗaliban da su fice daga harabar jami’ar.

Shugaban jami’ar ya ci gaba da cewa, an gaggauta tura jami’an tsaro ɗauke da makamai domin sintiri, sa ido da kuma tsaro, kuma an kama masu laifi da dama.

“Hukumar Jami’ar ta samu rahoto kan mutuwar Modupe Deborah Atanda wacce aka samu rahoton vatarta tun ranar Laraba, 6 ga Satumba, 2023; kuma jami’ar na alhinin mutuwar a halin yanzu,” inji sanarwar.

“Ya dace a gaggauta sanar da ɗaukacin al’ummar Jami’ar cewa an ɗauki matakin gaggawa kan wannan lamarin, saboda an tsara dukkan jami’an tsaro domin shawo kan lamarin. Hasali ma dai an kama wasu da ake zargi.

“Don haka, duk ɗalibai, ana umurtarsu da su fice daga harabar cikin gaggawa nan da nan don tabbatar da ingantaccen bincike, cikakke, kuma ba tare da cikas ba.

’Yana da kyau a san cewa an tura jami’an tsaro ɗauke da makamai cikin gaggawa domin yin sintiri, sa ido da kuma tsaro.

“Tabbas Jami’ar za ta ɗauki dukkan matakan da suka dace don kamo duk wani mai laifi; za su fuskanci cikakken sakamako na ayyukansu.

“Za a gabatar da sabon ranar dawowa ga duk ɗalibai. Muna matuƙar baƙin ciki duk wani rashin jin daɗi da wannan ya haifar. Na gode.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *