An yaba wa Gwamna Buni kan inganta harkokin noma da ayyukan raya ƙasa a Jihar Yobe

Daga GAMBO ISAH

Honorabul Zannah Babagana, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar Hukumar Bursari a Majalisar Dokokin Jihar Yobe a wata zantawa da ya yi da manema labarai a cikin satin nan, ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni bisa tallafa wa harkokin noma a jihar.

Honorabul Zannah ya ce, Gwamna Mai Mala Buni ya himmatu wajen bunƙasa harkar noma tare da ƙudirin kasafin kuɗin da aka ware domin bunƙasa noma a ƙananan hukumomi 17, inda ya buƙaci da a tsaya tsayin daka yi amfani da kasafin kuɗin da aka ware domin bunƙasa noma da tallafawa shugaban ƙaramar hukumar Honarabul Lawal Bukar Guba.

Honorabul Zannah Babagana ya kuma majalisar jihar ta 8  ta himmatu wajen gudanar da ayyukan da aka kafata, inda suka kafa dokar hukumar bunƙasa fasahar sadarwa ta jihar Yobe da kuma samar da Kwalejin Aikin Jinya da Unguwar Zoma ta Shehu Sule College of Nursing & Midwife da ke Damaturu, domin bayar da digiri a shirin a likitanci, aikin jinya da Ungozoma ga ɗalibai.

Honorabul Zannah ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta duba halin da jihar Borno ke ciki na rashin kyawawan hanyoyin da ke zama tarkon mutuwa, yana mai kira ga gwamnati a matakin biyu a matsayin wani abu mai muhimmanci ga jama’a na aikin samar da hanyoyi domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya shawarci matasan jihar da su kasance jakadu nagari, ta hanyar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi.

Ya yi kira ga iyaye da matasa da su riƙa yi wa shuwagabanninsu addu’a, domin samun romon dimokuraɗiyya.

Zannah ya miƙa godiyarsa ga hukumar NEDC bisa kyawawan ɗabi’u da suka ƙara ƙaimi wajen ci gaban al’ummar jihar Arewa maso Gabas, inda ya buƙace su da su ƙara ƙaimi a ƙarƙashin kyakkyawan jagoranci na mai girma Sanata Kassim Shettima, mataimakin shugaban Nijeriya.

Honorabul Zannah ya kuma jajenta wa al’ummar jihar Borno, gwamnati da Shehun Borno bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da ta addabi Maiduguri da ƙaramar hukumar Jere a jihar.