An yanke masa hukuncin shekara 2 a gidan yarin saboda harƙallar Kirifto Karansi a Legas

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai wata kotun laifuka na musamman dake Ikejan jihar Legas ta yanke hukuncin shekara biyu a gidan yarin ga wani ɗan kasuwar canji da aka kama da laifin harƙallar Kirifto Karansi wanda ya kai darajar Naira miliyan 20.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai Alƙalin kotun Mai shari’a, Oluwatoyin Taiwo ya yanke wa wani ɗan canji mai suna Shola Henry hukuncin zaman gidan kaso na shekaru biyu bayan saninsa da Laifuka iri-iri har guda biyu da kotun take tuhumasa da su.

Hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ita ce ta fara tuhumarsa shi da kamfaninsa mai suna Henry Enterprises ta kuma maka shi a kotu a kan wasu laifuffuka da suka haɗa da sata da kuma mallakar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.

Shi dai Henry an kama shi da laifin yaudarar wani Mista Anyasi Matthew wanda shi Henry ɗin ya yaudara a kan ya zuba hannun jari a harkar Kirifto na miliyan 20 wanda aka yi masa alƙawarin za a ba shi ribar kaso 20 na kuɗin bayan kwanaki 30 kacal.

Lauyan EFCC ya bayyana wa kotun cewa, bayan amsar waɗancan kuɗaɗen daga Misra Matthew, sai kuma ya yanke shi Henry ɗin a sabga, sannan ya kwata-kwata ma ya hana shi uwar kuɗinsa balle riba.

Wannan shi ya tilasta Mista Matthew ya kai Henry wajen hukumar EFCC don a bi masa kadinsa.

Alƙalin kotun ya bayyana cewa, ita wannan harka ta Kirifto Karansi ba komai ba ce illa laluben a cikin duhu. Amma duk da haka, ya tabbatar da laifin satar a kan wanda ake zargi. Sannan an nemi ya biya tarar Naira miliyan biyu, kamfaninsa kuma, miliyan guda. Sannan an ba shi wa’adin shekara guda don dawo da Naira miliyan ashirin ga wanda ya ha’inta.