An yanke mata hukuncin zama gidan yari bisa yaɗa bidiyon tsaraicin tsohon mijinta

Wata kotun majistare da ke zamanta a Ƙaramar Hukumar Minjibir a Jihar Kano ta tasa ƙeyar wata mata ’yar shekara 22 zuwa gidan gyaran hali sakamakon yaɗa bidiyon tsiraici na tsohon mijinta a kafar manhajar WhatsApp. 

Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun cewa, laifin ya saɓa wa sashe na 392 na kundin laifuffuka.

Yayin da ta ke mayar da martani kan tuhumar, matar da ake zargin, Nafisa Lawan, ta shaida wa kotun cewa ta sanya bidiyon ne a ɓangaren ‘status’ kuma yadda tsohon mijinta ne kaɗai zai gani, don haka babu wanda ya kalli bidiyon sai shi.

Ta ce, “kafin na saka bidiyon, na tabbatar na saita shi ta yadda shi kaɗai ne zai gani. Ban san yadda abin ya faru ba.”

Alƙalin kotun, Salisu Haruna Danbatta, ya umurci wanda ya shigar da ƙarar ya kawo bidiyon gaban kotu, da kuma waɗanda suka kalli bidiyon, sannan ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga watan Yuni.