An yanke wa mawaƙi R. Kelly hukuncin ɗaurin shekara 30 a gidan yari

Daga AISHA ASAS

Wata kotu a Amurka ta aike da shahararren mawaƙi R. Kelly gidan yari har na tsayin shekaru 30, kan samunshi da laifin cin zarafin mata da ƙananan yara ta fuskar jima’i.

Mai shari’a Judge Ann Donnelly ce ta zartar da hukuncin a Kotun Tarayya da ke Brooklyn, kusan shekara ɗaya kenan bayan kama mawaƙin da aikata laifin a garin New York.

R. Kelly na ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan R&B da duniya ta san da zamansu tare da ba su muhalli na musamman, kafin ya samu kansa a aikata wannan ɗanyen aiki ga ƙananin mata, wanda ya kai shi ga wannan hukunci.

Duk da cewa, R.Kelly bai zama mawaƙi a Amurka na farko da yake aikata irin wannan cin zarafin ga mata ba, sai dai hukuncin da aka yanke masa shine irinsa na baya-bayan nan da kotu ta zartar.