An yanke wutar lantarkin Jami’ar ABU ɗungurugum

Daga BELLO A. BABAJI

Hakan na zuwa ne sakamakon rashin biyan kuɗin wuta da Jami’ar ta Ahamadu Bello dake Zariya ta gaza yi.

Lamarin ya auku ne tun ranar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba inda Kanfanin raba wutar lantarki na Jihar Kaduna ya katse wutar jami’ar.

Acikin wata takarda da ABU ta fitar, ta bayyana wa malamai da ɗalibai cewa ta na iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta biya kuɗin wutar da ake bin ta.

Jami’ar ta shiga halin tsaka-mai-wuya ne tun farkon shekarar nan bayan da aka ƙara kuɗin wuta, kamar yadda ya ke ƙunshe a cikin takardar.

Premium Times ta ruwaito cewa Jami’ar ta kashe sama da Naira biliyan 1 tun daga farkon 2024 a kuɗin wuta banda na sayen gas da fetur dake amfani da su wa injinanta.

Jami’o’in Nijeriya da asibitocin koyarwarsu suna fuskantar matsalolin biyan kuɗin lantarki tun bayan ƙara kuɗin da Hukumar Lantarki ta Ƙasa, NERC ta yi a watan Afrilu.