An yaye sabbin ɗaliban fim a Kano

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

Bayan cigaban da makarantar koyar da harshen Turanci ta Jammaje Academy ta samu daga koyar da harshen Turanci zalla zuwa wasu kwasa-kwasai na koyar da sana’o’i da dabarun yin kasuwanci, a yanzu kuma makarantar ta fannin koyar da dabarun fitowa a fim, wato ‘acting’, ta kai ga matakin yaye ɗaliban da suka shiga cikin kwas ɗin a zango na farko.

A ranar Lahadi, 10 ga Oktoba, 2021, aka gudanar da taron yaye ɗaliban guda 40 tare da ba wa wasu daga cikinsu shaidar kammala karatun nasu da suka yi na tsawon watanni.

Taron, wanda aka gudanar da shi daga ƙarfe 7:00 zuwa 11:00 na dare a ɗakin taro na Kannywood TV da ke titin Muhammadu Buhari a cikin garin Kano, ya samu halartar manyan baƙi, musamman daga cikin shugabannin masu gudanar da harkokin sana’ar ta fim.

Tun da farko dai, da ya ke gabatar da jawabin manufar taron, shugaban makarantar, Malam Kabiru Musa Jammaje, ya ce, “shi wannan taron mun shirya shi ne, domin bikin yaye ɗaliban da suka samu horo a ajin koyar da ‘Acting’ wato koyar da yadda a ke harkar fim ta ɓangaren Jarumai wanda muka samar. Kuma wannan abin ya samo asali ne daga shekarar da ta gabata a sakamakon haɗuwar mu da fitaccen Darakta Ishak Sidi Ishak a lokacin taron qaddamar da wani littafi da na yi a kan koyon Turanci a Gidan Mambayya, shi ne ya bada shawara. To abin sai ya ba ni sha’awa saboda yana ganin samar da ajin koyar da dabarun ‘Acting’ yana da muhimanci saboda Matasa masu sha’awar shiga harkar fim suna da yawa, kuma suna buƙatar su yi ilimi a kan harkar, wanda kuma ya tabbatar da cewar zai iya bayar da gudummawar sa, to da wannan shawarar da ya ba mu ce muka samar da wannan ajin wanda a yanzu an kai ga samar da mutane da za a yi bikin yaye su da muka taru a nan a yanzu.”

Ya qara da cewar, “matakin karatun mun ware masa wata uku ne kullum sau ɗaya a sati, daga ƙarfe 2 zuwa 4. kuma muka samar da wani tsari da fitar da kwasa-kwasai guda uku wanda ni na ke koyar da ɗaya, Ali Nuhu ya ke koyar da ɗaya, sai shi Ishak Sidi Ishak ya ke koyar da ɗaya. Kuma sai muka rarraba a tsakanin mu, wannan zai zo a wannan rana, rana ta gaba kuma sai wani ya zo. To alhamdu lillahi dai a yanzu ga shi an samu sakamakon da a ke buƙata.”

Ya ci gaba da cewar “maganar gaskiya su ɗaliban sun nuna jajircewa saboda suna son abin sosai wanda a cikin 40 ɗin da muka koyar mun yaye 34 waɗanda su ne za mu ce sun yi nasara kuma mun yaba da ƙoƙarin su, sannan kuma bayan sun gama karatun sai da suka je aka yi gwaji wanda aka yi fina-finai guntaye guda uku domin su aiwatar da abin da suka koya, wannan ma ka ga nasara ce, wanda dukkan fina-finan nan gaba za mu saka su a shafin mu na ‘YouTube’ kowa ya gani. Sannan kuma wata nasarar da muka samu ita ce, wannan taron da mu ke na bikin yaye su don haka muna alfahari da wannan tsarin da muka samar wanda mu ke fatan zai samar da cigaba ga masana’antar fina-finai ta Kannywood da kuma samar da aikin yi ga Matasa.”

Shi ma da ya ke nasa jawabin. Mai unguwar Mandawari kuma ɗaya daga cikin Dattawa a masana’antar Kannywood Alhaji Ibrahim Mandawari ya bayyana Malam Kabiru Musa Jammaje a matsayin mai ƙoƙarin samar da ci gaba a cikin Matasa wanda a ƙoƙarin sa ne ya samar da wannan fanni na koyar da sana’ar fim wadda Matasa za su samu aikin yi tare da dogaro da kan su.”

Ya ci gaba da cewar, “muna godiya ga Allah da ya kawo mu wannan lokacin da sana’ar fim ta yi darajar da har za a samu wanda zai wani aji da za a koyar da ita wanda ba zan manta ba lokacin da muka yi ‘Aminu Mijin Bose’ Jarumar da ta fito a cikin fim ɗin da ta je gida babanta ya rufe ta da duka. Amma yanzu ga shi har an kai ga ana biyan kuɗi a koyi harkar fim.”

Daga qarshe ya yi kira ga waɗanda suka koyi harkar fim ɗin da cewar su sani sana’a suka koya don haka kada su yi wasa da ita. 

Shi kuwa a na sa jawabin, shugaban ƙungiyar Jarumai ta Jihar Kano Alhassan Kwalle, ya nuna farin cikin sa ga wannan tsari na makarantar Kabiru Musa Jammaje, wanda ya ce su ɗaliban da suka samu horo a makarantar a shirye muke mu karɓe su a matsayin jarumai da takardar sakamakon da suka samu.”

Shi ma fitaccen jarumi kuma Furodusa Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON a na sa jawabin ya yi kira ga waɗanda suka samu horon da kada su ɗauki kwalin da suka samu a matsayin shikenan sun samu harkar fim, dole sai sun bi wasu hanyoyi da za su samar musu da aikin, “kuma a matsayin mu na waɗanda suka san harkar a shirye mu ke da mu ba su duk wata gudummawar da su ke buƙata.”

Shugaban ƙungiyar kwararru ta masu shirya fim ta ƙasa MOPPAN Dakta Ahmad Sarari, shi ma ya hori jaruman da aka yaye da su zamo jakadu nagari wajen gudanar da abin da suka koya, domin a cewar sa harkar fim sana’a ce da ta ke samar da cigaba don haka sai su ɗauki abin da suka koya da muhimanci domin su samu cigaban da su ke buƙata. 

Su ma ɗaliban da su ka samu horon sun bayyana farin cikin su a bisa yadda suka gudanar da zaman ɗaukar darasin, kuma suka godewa Malamansu musamman shugaban makarantar Malam Kabiru Musa Jammaje bisa kulawar da ya ba su na ganin sun fahimci abin da a ke koyar da su. 

An dai kammala taron ne da cin abinci, bayan an kammala aka raba shaidar kammalawar ga ɗaliban tare da karrama wasu fitattun mutane da suka bayar da gudunmawar su ga ci gaban makarantar da kuma harkar fim.

A cikin waɗanda aka karrama a taron akwai jarumai irin su Ali Nuhu, Abba El-Mustapha, Nasir B. Muhammad, Ishak Sidi Ishak da sauransu.