Allah Ya yi wa Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan Ahmad Danbaba, rasuwa.
Wata majiya ta kusa da ahalin marigayin ta ce, marigayin ya rasu ne ran Asabar a Kaduna bayan fama da rashin lafiya.
Dangi, ‘yan’uwa da abokan arziki na kusa da nesa sun bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ba ga jihar Sakkwato kaɗai ba har ma da ƙasa baki ɗaya.
Tuni dai aka gudanar da jana’izar marigayin a Sakkwato daidai da karantarwar addinin Islama.