An yi jana’izar waɗanda suka rasu a iftila’in masallaci a Zariya

Daga BASHIR ISAH

Aƙalla mutum 10 ake fargabar sun riga mu gidan gaskiya sannan da dama sun jikkata sakamakon rikitowar wani ɓangare na ginin Babban Masallacin Zariya da ke Kaduna.

Da yake tabbaar da aukuwar iftila’in da ya auku a ranar Juma’a, Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce lamarin ya faru ne da la’assariyar wannan rana.

Ya ce, “Tun farko, jiya mun lura cewa bangon ginin ya tsage inda aka fara shirin ɗaukar injiniyoyin da za su yi aikin gyara kafin daga bisani wannan iftila’in ya auku.”

Bayan miƙa ta’aziyya ga ‘yan uwan waɗanda suka rasu a hatsarin, Basaraken ya ba da umarnin daga yanzu a ci gaba da gabatar da sallah a wajen masallacin kafin aiwatar da gayare-gyaren da da suka kamata.

Domin cika umarnin Sarkin, an gudanar da jana’izar marigayan da misalin ƙarfe 8:30 na ranar Juma’ar da hatsarin ya auku a fadar sarkin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *