An yi kiciɓis tsakanin Atiku da Tinubu a filin jirgi

Daga BASHIR ISAH

Jigo a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya tarbi Tsohon Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar a filin jirgi yayin da ya dawo daga hutun da ya tafi ƙasar waje.

Atiku Abubakar ya isa babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne da daddare a Juma’ar da ta gabata.

Atiku ya bar Nijeriya na tsawon lokaci inda ya tafi hutu a ƙetare.

A matsayinsa na ɗan hamayya, Atiku ba ya sanya wajen faɗin albarkacin bakinsa dangane da batutuwan da suka shafi ƙasa.

Sai dai babu wani ƙarin bayani kan ko haɗuwar jigogin biyu shiryayyen allamari ne ko kuma dai dama ce ta gitta.

Amma a bidiyon tarbar da aka yaɗa, an ga lokacin da ake raɗa wa Tinubu zuwan Atiku inda ya je ya same shi suka gaisa bayan ya sauko daga motarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *