An yi kira ga sabbin jami’an hana fasa ƙwauri 335 da aka yaye a Kano su zama jakadu nagari

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Kwalejin Horas da Jami’an Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa dake Gordon dutse a jihar Kano ta yaye sabbin jami’ai da suka kammala karvar horo guda 335.

Taron wanda ya samu baquncin mataimakin kwanturola na qasa mai kula da sashin bincike, Muhammad Abba Kurra.

Da yake jawabi mataimakin kwanturola janar na hukumar ya ce waɗanda aka yaye ɗin su zama jakadun hukumar a duk inda za a kaisu, aikinsu nagari zai ƙarawa hukumar daraja akasin haka kuma zai zubar musu da kima.

Ya yi kira gare su akan su yi aiki da doka da ƙa’ida ta hukumar a yayin gudanar da aikinsu ko ba a yayin da suke kan aiki ba, su sa a ransu su ma’aikatan hukumar hana fasa ƙwauri ne.

DCG. Muhammad Abba Kurra ya ja hankalin waɗanda aka yaye su cigaba da aiki tuquru da faɗaɗa karatunsu da yin amfani da irin darasussuka da suka koya ta aiwatar da shi ta hanyar da ya dace.

Tun da farko a jawabinsa na maraba kwanturola na kwalejin horas da jami’an na hana fasa ƙwauri, RA.

Adahunse ya ce waɗanda aka yaye sun sami horo daga 22 ga watan Maris zuwa watan Yuni 2023 watanni uku kenan.

Ya ce sun samu horo a darussa daban-daban. Sannan an yi musu jarrabawa akai sun sami nasara sannan sun shiga cikin harkokin gasa na wasanni daban-dadan da wasu suka sami lambobin yabo.

Kwanturola na Kwalejin Horas da jami’an hana fasa 2
Ƙwaurin na goron Dutse ya yi fatan waɗanda aka yaye za su yi aiki da ƙwarewa da suka samu a duk inda sami kansu.

Sannan ya yaba da irin gudummuwa da kwanturololin hukumar na shiyyoyi daban-daban suka basu, ya kuma gode wa dukkan malamai da ma’aikatan kwalejin.

R.A. Adahunsa ya yi kira jami’an da suka sami horo aka yaye su zama sun yi aiki da ƙwarewa da tarbiyya da suka samu a yayin ɗaukar horo a kwalejin.

A jawabinsa na godiya Mataimakin Kwanturola na kwalejin mai kula da darussa Idris Abaje ya gode wa dukkan mahalarta taron musamman manyan jami’an hukumar da manyan jami’an tsaro daban-daban da karramasu da halartar taron.

An raba lambar yabo ga jami’an a fannoni daban-daban ga waɗanda suka fi nuna ƙwazo a lokacin da ake ba su horo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *