An yi naɗe-naɗen manyan muƙamai a Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, sun yi naɗe-naɗe na manyan muƙamai a majalisar tarayya.

A yayin zaman majalisun a ranar Talata Akpabio da Abbas suka sanar da naɗe-naɗen sabbin manyan muƙaman da aka yi.

A Majalisar Dattawa, Akpabio ya ambaci Opeyemi Bamidele a matsayin Shugaban Masu Rinjaye, David Umahi a matsayin Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye; Mohammed Ali Ndume a matsayin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye, sai Lola Ashiru a matsayin Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu rinjaye.

Yayin da a Majalisar Wakilai kuwa, Abbas ya ambaci Julius Ihonvbere daga Edo a matsayin Shugaban Masu Rinjaye, dai kuma Abdullahi Ibrahim Halims daga Kogi a matsayin Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye.

Kazalika, Abbas ya ambaci Bello Usman Kumo daga Gombe a matsayin Babban Mai Tsawatarwa da Adewunmi Oriyomi Onanuga daga Ogun a matsayin Mataimakin Babban Mai Tsawatarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *