An yi nasarar daƙile haɗarin bazuwar COVID-19 a unguwannin Shanghai

Daga CMG HAUSA

Shugaban tawagar jami’an yaƙi da annobar COVID-19 na Shanghai, Gu Honghui, ya bayyanawa taron manema labarai cewa, an samu nasarar daidaita matsalolin haɗarin yaduwar annobar COVID-19 a unguwannin birnin Shanghai.

Gu, ya ce, adadin yaɗuwar cutar yana kara raguwa, yayin da alƙaluman suka ragu daga makin Rt 2.27 zuwa 0.67.

Makin Rt ya kan nuna yanayin saurin yaɗuwar cutar COVID-19.
A cewar Gu, adadin yana cigaba da raguwa da ƙasa da maki guda cikin kwanaki 15 a jere.

An samu adadi mafi yawa na sabbin masu kamuwa da cutar a Shanghai a ranar 13 ga watan Afrilu, wanda ya kai 27,605, tun daga wancan lokacin kuma, adadin yayi ta raguwa.

A ranar Asabar, an samu rahoton sabbin masu kamuwa da cutar kimanin 788 a birni na Shanghai.

Kawo yanzu, wannan babban birni mai matsayin cibiyar kasuwanci ta ƙasar Sin ya samu jimillar masu kamuwa da cutar COVID-19 53,364, tun daga ranar 26 ga watan Fabrairu, kana an tabbatar cutar ta hallaka mutane 422 a birnin.

Mai Fassara: Ahmad