An yi wa Hukumar Alhazai tunin maido da kuɗin adashin gata

Daga AMINA YUSUF ALI

A ƙoƙarinsu na ganin sun cikasa wannan damar da kundin mulki ya ba wa al’umma na   ‘yancin samun bayani, mawallafan jaridar Hajj Reporters sun aike wa da hukumar alhazai takardar tuni ga hukumar jin daɗin alhazai domin su ba da ƙarin bayani a kan batun maido kuɗaɗen aikin hajji ga alhazan da suka biya kuma ba su samu damar tafiya ba a shekarun 2020/2021.

Da ma ba wannan ne karo na farko da kamfanin jaridar yake aike wa da hukumar makamanciyar irin wannan wasiƙa ba, amma har yanzu shiru ba amsa.

Waɗannan jawabai suna ƙunshe ne a wata wasiƙa wacce shugaban tsare-tsare na jaridar Hajj Reporters ɗin, (IHR) Ibrahim Muhammad ya rubuta ranar Larabar da ta gabata, sannan kuma ya sanya mata hannu.

A cikin takardar wacce aka aike ta ranar 11 ga watan Agustan Shekarar nan da muke ciki, an yi waiwaye a kan takardar farko da kamfanin ya aike wa da hukumar tun a ranar 30 ga watan Yunin shekarar nan. Inda wasiƙar take ƙunshe da tuni ga hukumar alhazai a game da ba da cikakken bayani a kan maniyyatan hajjin shekarar 2020/2021 wanda aka soke saboda dokar hana zirga-zirga. Kuma a cikin wasiƙar an bayyana cewa, sassa na 1 da na biyu na dokar ‘yancin samun bayanai shi ya ba su damar neman waɗannan bayanai.

Inda kamfanin ya bayyana cewa an aike da waɗancan wasiƙu i zuwa ga jihohin Kaduna, Adamawa, Niger, Kogi, Bauchi, Kwara, Sokoto, Kebbi, Borno, Zamfara, Legas da Taraba.

Bayanan da kamfanin ya nema sun haɗa da,  jimillar adadin alhazan da suka yi rajistar aikin hajji a shekarun 2020 da 2021 daga kowacce jiha.

Ta biyu ita ce, jimillar adadin maniyyatan aikin hajjin na 2021 da 2021 da aka mayar wa da kuɗaɗensu, sai kuma adadin alhazan da suka amince su yi ciko a kan kuɗin da suka biya a baya, su biya hajjin shekarar da muke ciki.
Jimillar adadin maniyyatan aikin hajji na 2021 da kuma ƙiyasin  ku]in kafin alƙalamin da kowannensu ya zuba.

Jimillar adadin maniyyatan aikin hajjin da suka shiga adashi don biyan hajji da kuma adadin kuɗin da kowannensu ya biya.

Jimillar adadin kuɗaɗen da maniytatan suka biya a hukumar alhazan a watan Yunin shekarar 2020?
Sunayen bankunan da aka yi hada-hadar biyan hajjin.

Ita dai dokar ‘yancin samun bayani, doka ce da aka yi ta a shekara ta 2011. Kuma an yi ta ne don samun damar fitar da mutane daga duhu da ruɗani na wasu al’amura da hukumomi masu zaman kansu da kuma na gwamnati suke gudanarwa.