An yi wa Kakakin ‘Yan Sanda na Katsina da wasu ƙarin girma

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘Yan Sanda ta Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Usman Baba Alƙali, ta ƙara wa wasu jami’anta shida girma a Katsina ciki har da Kakakin rundunar na jihar, Gambo Isa.

Ƙarin girman ya haɗa da wasu jami’ai uku da aka ɗaga darajarsu daga muƙaman Sufurtandan ‘Yan Sanda (CP) zuwa Babban Sufurtandan ‘Yan Sanda ( CSP).

Sauran da lamarin ya shafa su ne, Aliyu Sale, Iliyasu Usman Bugaje da kuma Peter Daniel.

An gudanar da bikin ƙarin girman ne a ofishin ‘yan sanda da ke Kangiwa Road, G.R.A, Katsina.

Haka zalika, manyan jami’an rundunar biyu, wato Ibrahim Abdul (DCP) da kuma Musa Hamza Yusfari (ACP), sun sami ƙarin girma zuwa DCP da ACP.

Bikin ya samu halartar shugabannin rundunonin tsaro da suka haɗa da Hukumar Shige da Fice, Hukumar Kare Haɗurra, Hukumar Tsaron Farin Kaya da dai sauransu.