Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gabannin zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Katsina, hukumar NDLEA ta gudanar da gwajin ƙwaƙwalwa ga yan takarar kujerar shugabancin ƙaramar hukuma a jihar.
kwamandan hukumar hana sha da fatauci miyagun ƙwayoyi a Jihar Katsina, Mohammed Aminu Abubakar ya bayyana haka da yake hira da manema labarai a ofishin sa.
Ya ce wannan gwaji na ƙwaƙwalwa ya gudana ne da haɗin gwiwa da hukumar zaɓe (INEC) da kuma gwamnatin Jihar Katsina da ita hukumar hana sha da fatauci na miyagun ƙwayoyi.
Yan takarar kujerar shugabanin ƙaramar hukuma 533 suka yi gwajin ƙwaƙwalwa da hukumar NDLEA ta shirya.
Kwamandan yayi bayani kan nasarorin da hukumar ta samu a shekarar da ta wuce inda ya sanar da kama mutane 734 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
“Haka kuma cikin waɗanda hukumar ta kama, mutane 253, kotu ta yanke masu hukunci a laifuka daban daban,sai mutane 107 cikin masu laifin, suna gaban bubban kotun tarayya suna fuskantar tuhuma daban daban”kwamandan ya bayyana haka.
Aminu Abubakar ya ƙara da cewa hukumar ta kuma kama haramtattu kwayoyi masu nauyin kilogram 1,525 da suka haɗa da hodar Ibilis (cocaine) da ganyen Wiwi,tramoil da sauran su.
Kwamandan ya bayyana ƙoƙarin da hukumar ta yi wajan gudanar da shirye shirye da tarurruka kan illar ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.
“A shekarar da ta wuce mun shirya tarurruka 155 na ƙarawa juna sani da wasu shirye shirye kan illar ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar “inji kwamandan NDLEA a jihar.
Ya nuna godiyar sa ga gwamna Dikko Raɗɗa akan irin goyon baya da taimakon da yake baiwa hukumar bisa ƙoƙarin da take na magance matsalar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.
Kwamandan ya kuma yabawa masu ruwa da tsaki da suka haɗa da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin sa kai akan goyon baya da suke ba hukumar.
Ya sha alwashin ganin jami’an hukumar NDLEA a jihar sun kawo ƙarshen safarar miyagun ƙwayoyi zuwa jihar.