An yi zirga-zirgar da ta haura miliyan 400 yayin bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin na bana

Daga CMG HAUSA

Ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa ta ƙasar Sin, ta ce bisa alƙaluman ƙididdiga, adadin zirga-zirgar da aka yi a cikin gida, yayin bikin ranar tunawa da kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin ta bana, ta kai miliyan 422.

Kuma cikin ranakun hutun mako guda na wannan biki, an tattara kuɗaɗen shiga da yawan su ya kai kuɗin Sin RMB yuan biliyan 287.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 40.45.

Alƙaluman sun nuna yadda a yayin hutun, masu yawon bude ido suka fi yin gajerun tafiye-tafiye, yayin da masu shakatawa na cikin gida suka fi ziyartar lambunan shan iska na wajen birane, waɗanda suka ɗauki kaso 23.8 bisa dari, da ƙauyukan dake kewaye da birane da kaso 22.6 bisa dari, da manyan wuraren shan iska da suka ɗauki kaso 16.8 bisa ɗari cikin jimillar wuraren da aka fi ziyarta.

Ma’aikatar sufurin ƙasar Sin ta ce ta yi hasashen karɓar fasinjoji masu tafiye-tafiye, da yawan su ya kai miliyan 255.54, a yayin ranakun hutun na mako guda na wannan biki.

Fassarawar Saminu Alhassan