An zaɓi Nasiru Mera a matsayin mataimakin shugaban majalisar malamai na ɗaya

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Ƙungiyar Izala da ke da shalkwata a Kaduna reshen Ƙaramar Hukumar Mulki ta Argungu da ke Jihar Kebbi ta zaɓi Malam Nasiru Abubakar Mera a matsayin mataimakin shugaban majalisar malamai na 1.

Shugaban majalisar malaman Sheikh Suleman Bawa ya bayyana cewa zaɓen Malam Nasiru Abubakar Mera ya biyo bayan la’akari ne da irin gudummawar da ya ke bayarwa wajen da’awa da kuma sauran hanyoyi wajen yaɗawa da ɗaukaka addinin Musulunci.

Sabon mataimakin shugaban majalisar malaman ya jaddada cigaba da bayar da duk gudummawar da ya yi wajen ɗaukaka addinin Musulunci tun kama daga da’awa ya zuwa ayyukan ƙungiya a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Duk da ya ke akwai malamai masu yawan shekaru fiye da shi amma aka yi nazarin zaɓensa wannan ba shakka ya ƙara zaburar da shi wajen aiwatar da ayyukan da ya ke na wajen da’awa.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi musamman ‘ya’yan wannan ƙungiyar da su cigaba da bai wa majalisar malamai haɗin kai saboda ita ce cibiyar aiwatar da kowane aiki na addini tun kama daga gudanar da wa’azi, tsarin karance-karance da makarantu.

Haka zalika kada su yi ƙasa a gwiwa wajen bayar da shawarwari a duk lokacin da suka ga wani abu da ya kamata a yi gyara a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *