An zaɓi Tinubu a matsayin sabon shugaban ECOWAS

An zaɓi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon Shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

Wannan ya faru ne yayin taron ƙungiyar karo na 63 wanda ya gudana a Guinea Bissau a ranar Lahadi.

Wannan ne karo na farko da Tinubu ya halarci taron na ECOWAS tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya karɓi bakuncin Shugaba Embalo a birnin Legas, inda ya ce sun ci abinci tare kuma “mun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafe mu.”

A wancan lokacin, Tinubu ya ce babban burinsa shi ne ya sake mayar da ƙasar jagora ga sauran ƙasashen nahiyar Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *