An zaɓi Xi Jinping a matsayin babban sakataren kwamitin ƙolin JKS

Daga CMG HAUSA

An zaɓi Xi Jinping, a matsayin babban sakataren kwamitin ƙolin Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20, yayin zaman farko na kwamitin da ya gudana Lahadin nan, kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwar bayan taron.

Zaman wanda Xi ya jagoranta, ya samu halartar mambobi 203 na kwamitin kolin JKS na karo na 20 da kuma mambobi masu jiran gadon wani muƙami 168.

Haka kuma a yayin wannan zama, an bayyana Xi a matsayin shugaban hukumar ƙolin sojojin kwamitin ƙolin JKS.

Mambobin zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin ƙolin JKS da aka zaɓa a zaman taron, sun haɗa da Xi Jinping, da Li Qiang, da Zhao Leji, da Wang Huning, da Cai Qi, da Ding Xuexiang, da Li Xi.

Bugu da kari, a yayin taron, an zaɓo mambobin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, wanda kuma ya amince da mambobin sakatariyar kwamitin kolin JKS da zaunannen kwamitin hukumar siyasa na kwamitin kolin JKS ya gabatar.

Zaman taron ya kuma sanar da sunayen mambobin kwamitin soja na kwamitin tsakiya na JKS.

Haka kuma zaman ya amince da sakatare da mataimakan sakatarori da mambobin zaunannen kwamitin hukumar ladabtarwa wato CCDI ta kwamitin ƙolin JKS, da aka zaba a yayin cikakken zama na farko na hukumar CCDI karo na 20.

Mai fassara: Ibrahim