An zargi Gwamnan Ribas da nuna wariya ga cigaban kasuwancin ‘yan Arewa

Daga HABU ƊAN SARKI

Ƙungiyar haɗin kan marubuta a kafafen sada zumunta na Soshiyal Midiya, ta Arewa Media Writers ta bayyana damuwa game da ƙalubalen da Hausawa mazauna Jihar Ribas ke fuskanta na rusa harkokinsu na kasuwanci da ƙuntata wa rayuwarsu da suke zargin Gwamnan jihar Nyeson Wike da sa hannun a ciki.

A cikin saƙon da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamred Abba Sani Pantami ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta koka da irin ƙuntatawar da ta ce Gwamnan Jihar na yi wa ‘yan Arewa mazauna jihar, musamman biyo bayan rushe kasuwar da ‘yan Arewan suke harkokinsu fiye da shekaru 40 da suka gabata, duk kuwa da yadda suke kiyaye dokokin jihar da biyan haƙƙoƙin da ake sanya musu.

Shugaban ƙungiyar Arewa Media Writers na Jihar Ribas, Malam Murtala Adam, ya ce tun daga watan Maris na shekarar da ta gabata lokacin da aka rufe kasuwanni sanadiyyar cutar COVID-19, Gwamnan ya sa aka daina harkoki a kasuwar, duk kuwa da kasancewar sauran kasuwannin jihar an sake buɗe su daga baya.

Zargin da ‘yan Arewa mazauna birnin Fatakwal ke yi shi ne na Gwamnan Jihar na nuna musu wariya da tauye haƙƙi a matsayin su na ‘yan Nijeriya, duk kuwa da kasancewar kasuwar da suke harkokin su a ciki mallakin Gwamnatin Tarayya ce.

A dalilin rusa wannan kasuwa ne dai yanzu haka, a cewar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Kwamred Abba Sani Pantami, mutane da dama suka shiga wani mummunan hali, wasu sun gamu da lalurar hawan jini da shanyewar wasu gaɓoɓin jiki, wasu ma har sun rasu, saboda ƙunci da baƙin cikin lalata musu dukiya da gwamnatin jihar ta sa aka yi.

Ƙungiyar ta nemi Gwamnatin Tarayya, Majalisar Gwamnonin Arewa, ministoci ‘yan Arewa, sanatoci da ke wakiltar yankin Arewa, ‘yan majalisun jihohin Arewa da sauran masu faɗa a ji na yankin Arewa da su kai wa al’ummar Arewa da ke zaune a yankin ɗaukin gaggawa.