Ana barazana da rayuwata saboda ƙin goyon bayan tsige Mahdi, cewar ɗan majalisar Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Salisu Usman, wanda shi kaɗai ne ba ya goyon bayan a tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara, ya ce ya yi gudun hijira daga Zamfara, saboda yunƙurin da “gwamnatin jihar ke yi domin ta cim min don na ƙi goyon bayan a tsige mataimakin gwamna.”

Usman dai shi kaɗai ne ba ya goyon bayan tsigewar, kuma shi kaɗai ne ɗan majalisar da ya rage a PDP, sauran duk sun bi Gwamna Bello Matawalle zuwa jam’iyyar APC.

Ya ƙi halartar zaman majalisa na makon jiya, inda mambobi 18 daga cikin 22 su ka halarci taron, kuma duk suka amince a tsige Mataimakin Gwamna Mahadi Aliyu.

Da yake bayani ga Sashen Hausa na BBC, Usman jami’an gwamnatin Zamfara na tsaro sun tashi haiƙan domin damƙe shi.

“Su na bibiya ta. Na san ƙoƙari suke yi su kama ni, saboda sun san zan iya daƙile ƙoƙarin su na tsige mataimakin gwamna.

“Idan sun kama ni ban san irin cajin da za su yi min ha. Amma dai Ni na san rayuwa ta na cikin hatsari. A yanzu dai na bar masu jihar.”

An tambaye shi ta yaya shi kaɗai zai iya hana a tsige Mataimakin Gwamna? Sai ya ce saboda gwamnati ta san ya fara canja wa wasu ‘yan majalisar ra’ayi, sun fara dawowa daga rakiyar goyon bayan a tsige mataimakin gwamna.

Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Matawalle, mai suna Zailani Bappa, ya ce zargin da Usman ya yi wa Gwamnatin Jihar Zamfara ba gaskiya ba ce, ƙirƙira ce kawai ya yi. ‘Yan Majalisar Jihar Zamfara su 18 daga cikin 22 ne suka kaɗa ƙuri’ar amincewa a tsige Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu.

Lamarin na zuwa ne kwanaki uku bayan da majalisa ta aike wa Mahdi Aliyu sammacin sanar da shi ya aikata laifukan da suka ce ya cancanci tsigewa.

Jihar Zamfara na neman afkawa cikin ruɗanin siyasa, bayan bala’in kashe-kashe da garkuwa da su ke fama da shi, yayin da Majalisar Jiha ta aika wa Mataimakin Gwamna Mahdi Shehu jerin laifukan shirin tsige shi.

Hakan ya faru ne a ranar Litinin, kwanaki uku bayan da majalisa ta karɓi buƙatar neman tsige Mahdi, wanda ya yi zaman sa a PDP, ya ƙi bin Gwamna Matawalle canja sheƙa daga PDP zuwa APC.

Mataimakin Shugaban Majalisa Musa Bawa ne ya miƙa tulin takardun bayanan da ke ƙunshe da laifuka da buƙatun tsige Mataimakin Gwamna.

Bawa wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin ya nemi a tsige Mahdi daga kujerar sa ta mataimakin gwamna.

Cikin wata sanarwar da Shamsuddeen Basko ya sa wa hannu, wadda kuma an aika ta ga Mataimakin Gwamna ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, takardar ta sanar da Mahdi cewa “mun cika sharuɗɗan da Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya amince, cewa 1/3 na Mambobin Majalisar Jiha sun amince da tsige ka.

“To Majalisa a ƙarƙashin Kakakin Majalisa ta amince da wannan sanarwa kamar yadda doka ta tanadar.

“Lokacin da muka gayyace ka a cikin 2021, sai ka ƙi zuwa, ka garzaya kotu. Kuma a lokacin ba mu da niyyar tsige ka, kamar yadda aka riƙa yaɗawa. Ya ce majalisa kuma a lokacin ta bi umarnin da kotu ta bayar.

Cikin laifukan da su ke zargin Mahdi ya aikata, akwai laifin keta alfarmar ofishin sa na Mataimakin Gwamna ta hanyar amfani da ofishin ya azurta kan sa da kuma kasa yin ayyukan sa na ofis a matsayin sa na Mataimakin Gwamna.

A zaman da Majalisa ta yi na ranar Alhamis ne mambobi uku na APC waɗanda ba su halarci zaman ba, su kaɗai ne ba su amince da tsige Mataimakin Gwamna ba. Sai kuma Mamba ɗaya na PDP, Salihu Usman mai wakiltar Mazaɓar Zurmi ta Arewa, wanda shi ma bai halarci zaman na ranar Alhamis ba. Kuma dama shi kaɗai ne ba ya goyon bayan tsige Mataimakin Gwamna Aliyu.

A hannu guda kuma Alƙalin-alƙalai ta Jihar Zamfara Mai Shari’a Kulu Aliyu ta rantsar da kwamatin mutum biyar da zai binciki laifukan da ake zargin Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu Gusau na rashin ɗa’a.

Kwamatin ƙarƙashin tsohon Alƙali Tanko Soba, an kafa shi ne sakamakon damar da kundin tsarin mulki ya ba wa alqalin, a cewar Mai Shari’a Kulu.

Ta ƙara da cewa Sashe na 185(5) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ne ya ba ta damar kafa kwamatin sakamakon buƙatar da Majalisar Dokokin Zamfara ta gabatar mata ranar 10 ga watan Fabarairu ta ƙorafi kan mataimakin gwamnan.

A gefe guda kuma, Babbar Kotun Abuja ta saka ranar 10 ga watan Maris don fara sauraron ƙarar da Mahdi Gusau ya shigar yana neman kotun ta dakatar da yunƙurin tsige shi da ‘yan majalisar ke yi, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ne ya ɗaga zaman a ranar Talata, yana mai umartar ɓangarorin su kimtsa kafin ranar ci gaba da shari’ar.