Ana buƙatar yin shawarwari maimakon rura wutar rikici idan ana son daidaita rikicin Ukraine

Daga CRI HAUSA

Halin da ake ciki a ƙasar Ukraine, ya samu babban sauyi a jiya Litinin, inda ƙasar Rasha ta sanar da amincewarta ga ‘yancin kan “Jamhuriyar Lugansk (LPR)” da “Jamhuriyar Donetsk (DPR)”, a matsayin ƙasashe masu cin gashin kansu dake gabashin Ukraine, matakin da ya jawo ƙaƙaba takunkumin kuɗi daga ƙasar Amurka da sauran wasu ƙasashen yammacin duniya ga Rasha.

A yayin taron gaggawa da kwamitin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ya kira dangane da batun Ukraine, ƙasar Sin ta yi kira ga ɓangarorin masu ruwa da tsaki da su nuna haƙuri, da kaucewa ɗaukar duk wani matakin da zai iya rura wutar rikici.

Akwai dalilai da dama, da suka jawo taɓarɓarewar halin da ake ciki a Ukraine. Ita dai Amurka ta zama mai hura wutar rikicin. Kwanan nan, Amurka ta riƙa tallata labaran da suke bayyana cewa, wai Rasha za ta mamaye Ukraine, a wani ƙoƙari na sake dawowa da goyon-bayan al’ummar ƙasar ga gwamnatin Biden, da taka birki ga ci gaban Turai da sauransu.

Amma idan ana son lalibo bakin zaren daidaita rikicin Ukraine, ya dace a zauna a yi shawarwari, maimakon rura wutar rikici. A matsayinta na zaunanniyar ƙasa dake kwamitin tsaron MDD, matsayin ƙasar Sin kan batun Ukraine bai sauya ba, wato ya kamata a mutunta kulawar duk wata ƙasa, da kiyaye ƙa’idoji gami da manufofin kundin tsarin mulkin MDD.

Ya dace ɓangarori masu ruwa da tsaki, su nuna haƙuri, don hana ta’azzarar halin da ake ciki a Ukraine. Ya kamata ƙasar Amurka da sauran wasu ƙasashe su taimaka ga yin shawarwari, maimakon tada zaune-tsaye. Ya dace manyan ƙasashe su zama kyawawan misalai, na gina duniya mai kyau.

Fassarawa: Murtala Zhang